mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

INA FAMA DA RASHIN SAMUN TABBATA CIKIN SAUKE WAJIBAI

Salamun Alaikum
Ina fatan Akaramakallahu zan fa’idantar da ni cikin wannan mas’alar: hakika ina rayuwa cikin rashin samuwa dorewa cikin sauken wajiban da suke wuyana daga ibada kai har da da ayyukan mustahabbi, wani lokacin sai na maida hankali kamar zan dore amma sai in dawo in watsar tareda cewa ni ina fatan cewa a kowanne lokaci ace na kasance cikin halin neman kusancin Allah Azza wa Jalla, hanya zuwa gareshi tana da tsayin gaske sannan kuma akwai tuntube da kayoyi cikin masu yawan gaske, hakika zunubi yana nesantar dani daga ubangijina, ina da yakini daga haka gashi kuma ruhina na mai da ni baya hakika wannan al’amari ya gajiyar da ni matukar gaske ina tuba in nemi gafarar ubangiji amma kuma sai na kara komawa kan aikata zunubin, shin ko akwai wata hanya da zata taimaka mini in samu tsayuwa kan da`ar Allah? Shin zaku taimaka mini zuwa ga hakan.
Allah ya jikan jujjuyawar yanayinmu da naku … Allah yayi muku taufiki.

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Hakika ya zo cikin hadisan Aklak cewa zuciya ta na yanayi biyu gabata da juya baya idan ta gabato to yi kokari ka dora kan aikin mustahabbi idan kuma ta juya baya to ka wadatu da sauke wajibai wannan na daga cikin yanayi da yanayiyyikan masu ibada, abu ne na dabi’a matukar dai yana sabon Allah matsarkaki, hakika mafi yawan bautar cikin mutane shine wanda yake sauke wajibai farillai ka da ka dbe tsammani daga rahamar Allah mayalwaciya lallai ita tafi yalwata daga zunubanmu sai dia cewa mai aikata sabo yana haramtuwa daga samun wasu darajoji madaukaka, shi koma kan sabo bayan tuba da kara tuba abu ne mai kyawu matukar dai bai kai ga komawa ga yin izgilanci da nafsu ba, ma’ana ya aikata zunubi sai ya yi istigfari da fatar harshe amma zuciyarsa tana nan kan begen zunubin kuma bai yi nadama ba sai ya kara maimaita wannan zunubi kamar misalin mummunar al’adar istimna’i wa’ayazubillahi, dole ne a tuba ga Allah tuba na hakika lallai Allah da manzonsa da Muminai suna ganin ayyuka, ka ji tsoran Allah lallai shi mai tsananin ukuba ne a muhallin azaba da ukuba.

Wurin ubangiji muke neman taimako.

Tarihi: [2019/10/21]     Ziyara: [477]

Tura tambaya