mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

MENE NE INGANCIN WANNAN RIWAYA


Salamu Alaikum.
Wannan riwaya da za ta zo ta zo cikin littafin Biharul-Anwar
Mene ne martaninku Allah ya saka muku da alheri
Sannan mene ne ingancin riwayar

Cikin Biharul-Anwar J 47 sh 356, babin tarikul Imam Jafarul Sadik (a.s)

Salamu Alaikum.

Wannan riwaya da za ta zo ta zo cikin littafin Biharul-Anwar

Mene ne martaninku Allah ya saka muku da alheri

Sannan mene ne ingancin riwayar

 

Cikin Biharul-Anwar J 47 sh 356, babin tarikul Imam Jafarul Sadik (a.s)


عن جعفر بن محمد ( ع ) انه قال : ود علي بن ابي طالب عليه السلام انه بنخيلات ينبع يستظل بظلهن وياكل من حشفهن ولم يشهد يوم الجمل ولا النهروان . وحدثني به سفيان عن الحسن قال ابو عبد الله ( ع ) زدنا : قال حدثنا عباد عن جعفر بن محمد انه قال : لما راى علي بن ابي طالب ( ع ) يوم الجمل كثره الدماء " قال لابنه الحسن " يا بني هلكت " قال له الحسن يا ابت اليس قد قد نهيتك عن هذا الخروج فقال علي ( ع ) ي بني لم ادر ان الامر يبلغ هذا المبلغ فقال له ابو عبد الله ( ع ) زدنا
قال : حدثنا سفيان الثوري عن جعفر بن محمد ( ع ) ان عليا ( ع ) لما قتل اهل صفين بكى عليهم ثم قال " جمع الله بيني وبينهم في الجنه

 

An karbo daga Jafar ibn Muhammad (a.s) cewa yace: Aliyu ibn Abu Dalib ya yi kaunar cewa ya samun kansa cikin gonar bishiyoyin dabino ya sha inuwarsu ya ci daga `yayan dabinonsu ya zama ace ma bai halarci yakin Jamal da yakin Naharawan ba. Sufyanu ya zantar da ni shi daga Hassan yace Abu Abdullahi (a.s) ka kara mana: yace: Ubbadu ya zantar da mu daga Jafar ibn Muhammad cewa shi yace: yayin da Aliyu Ibn Abu Dalib (a.s) ranar yakin Jamal ya ga yawan rayukan da aka rasa sai ya cewa da `dansa Hassan ya `dana na halaka” sai Hassan (a.s) yace masa ya babana ashe ban haneka daga wannan yaki ba sai Ali (a.s) yace: ya `dana ai ban san cewa lamarin zai kai ga haka sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce masa kara mana.

Sai yace: Sufyanu Assauri ya zantar da mu daga Jafar ibn Muhammad (a.s) cewa Ali (as) lokacin da aka kasha mutanen Siffaini yayi musu kuka yace ya Allah ka hada tsakaninmu ka tattara mu a cikin aljanna.

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Wannan Magana ce irin ta Umayyawam ina ai shi Sarkin muminai Ma’asumi ne da Ismar Allah mafi girma, bai aikata abinda ya aikata ba face da umarnin Allah maganar cewa Imam Hassan ya rubuta masa wasika ya hana shi wannan yaki wannan na daga cikin abinda yake shiryarwa zuwa ga gurbata da rashin ingancin riwayar a cikin mataninta ballantana batun isnadinta, mawallafin littafin Bihar-Anwar Allah ya tsarkake ruhinsa kamar yanda ya fadi a mukaddimar littafinsa lallai shi ya tattaro hadisai ne ingantattu da wadanda basu inganta ba daga misalsalan wadannan hadisai domin a san yanda masu kagar hadisan karya suka kagi hadisan, sun kasance suna damfara hadisai kan harshen A’imma tsarkaka (a.s) kamar yanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:  

سيكثر من بعدي الوضاعون الكذابون الذين يضعون الحديث عليّ كذباً

Da sannu makaga da makaryata zasu yawaita a bayana wadanda zasu dinga kagar hadisi a kaina bisa karya.

Hakan lamarin yake kan A’imma amincin Allah ya kara tabbata a garesu , matanin wannan hadisi na nuni da cewa na karya ne daga malaman Umayyawa ya gangaro masu batarwa masu danfara kiyayya ga Sarkin Muminai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi don suka da aibata shi cikin yakunansa da kuma cusa munafunci da karya kamar yanda Annabi (s.a.w) ya bashi labari da cewa bayansa akwai wadanda zasu tauye bai’arsa ma’ana Dalha da Zubairu  da Azzalumai ma’ana Mu’awiya da mabiyansa da masu fita daga addini ma’ana Kawarijawa da suka yake a yakin Naharawan 

Tarihi: [2019/10/19]     Ziyara: [477]

Tura tambaya