فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah

 

عن مولانا زين العابدين الإمام عليّ بن الحسين، قال  :

«وحقّ الصلاة أن تعلم أنّها وفادة إلى الله عزّ وجلّ ، وأنّک فيها قائم بين يدي الله عزّ وجلّ ، فإذا علمت ذلک قمت مقام الذليل الحقير، الراغب الراهب ، الراجي الخائف ، المستكين المتضرّع ، والمعظم لمن كان بين يديه بالسكون والوقار، وتقبل عليها بقلبک وتقيمها بحدودها وحقوقها».

89- daga shugabanmu Imam zainul abidin Ali bn Husaini (as) ya ce: (hakkin sa ne ka san cewa lallai ita liyafa ce zuwa ga Allah mai girma mabuwayi, lallai kan cikin sallah kana tsaye ne gaban Allah, idan ka san haka to zaka tsaya irin tsayuwar kaskantacce wulakantacce mai kwadayi da tsoro da gani girman Allah da fata da razana matsiyaci mai magiya, mai girmama wanda yake tsaye gabansa da nutsuwa da girmama, sannan ka fuskanci sallah da zuciyarka kuma tsayar da ita da iyakokinta da hakkokinta.

قال مولانا الإمام الصادق  7 :

«إذا استقبلت القبلة فانسَ الدنيا وما فيها، واستفرغ قلبک عن كلّ شاغل يشغلک عن الله، وعاين بسرّک عظمة الله، واذكر وقوفک بين يديه يوم تبلو كلّ نفسٍ ما أسلفت وردّوا إلى الله مولاهم الحقّ ، وقِف على قدم الخوف والرجاء، فإذا كبّرت فاستصغر ما بين السماوات العلى والثرى دون كبريائه ، فإنّ الله تعالى إذا اطّلع على قلب العبد وهو يكبّر وفي قلبه عارض عن حقيقة تكبيره قال  : يا كاذب ، أتخدعني ؟ وعزّتي وجلالي لاُحرمنّک حلاوة ذكري ، ولأحجبنّک عن قربي والمسارّة بمناجاتي .

90- shugabanmu Imam Sadik (as) ya ce: (idan ka fuskanci kibila ka manta da duniya da duk abin da yake cikinta, ka karkade zuciyarka daga dukkanin wani shagali da zai shagaltar dakai daga barin Allah, ka ga girman Allah da sirrinka, ka tuna tsayuwarka gaban Allah ranar kowanne rai ake jarrabarta da abin da ta gabatar akai mayar da su zuwa ga Allah ubangijin su na gaskiya, ka tsayu kan diga digin tsoro da fata, idan kai kabbarar harama to ka ga rashin girman dukkanin abin da ke tsakanin sammai madaukaka da kasa koma bayan girmansa, lallai Allah madaukaki idan ya tsinkayi zuciyar bawa lokacin da yake kabbara alhalin cikin zuciyar akwai wani abu da yake bijirewa daga hakikanin kabbarar sa sai Allah ya ce masa: ya kai makaryaci shin kana tsammanin zaka yaudareni ne? na rantse da buwayata da girmana lallai sai na haramta maka dadin ambatona, lallai sai na hijabanceka daga kusanta ta da farin cikin ganawa dani).

Ka sani cewa lallai shi Allah ba mabukaci bane zuwa ga hidimtawarka, lallai shi mawadaci ne daga bautarka da addu'arka, kadai dai ya kiraka ne da falalar sa domin ya yi maka rahama ya kuma nesantaka daga ukubar sa. 

ـ سئل بعض العلماء من آل محمّد  : فقيل له : جعلت فداک ، ما معنى الصلاة في الحقيقة ؟ قال  :

«صلة الله للعبد بالرحمة ، وطلب الوصال إلى الله من العبد إذا كان يدخل بالنيّة ويكبّر بالتعظيم والإجلال ، ويقرأ بالترتيل ، ويركع بالخشوع ، ويرفع بالتواضع ، ويسجد بالذلّ والخضوع ، ويتشهّد بالإخلاص مع الأمل ، ويسلّم بالرحمة والرغبة ، وينصرف بالخوف والرجاء، فإذا فعل ذلک أدّاها بالحقيقة ».

91-an tambayi ba'arin wasu malamai daga iyalan Muhammad (as), sai aka ce masa: raina fansarka, mene ne ma'anar sallah a hakika? Sai ya ce (sadarwar Allah ga bawa da rahama, da kuma neman danganewa zuwa ga Allah daga bawa idan ya kasance yana shiga da niyya yana kabbara da girmamawa da girma, yana karatu da jerantawa, yana ruku'u da kankan da kai, yana dagowa daga ruku'u da tawali'u, yana yin sujjada da kaskantar da kansa mika wuya, yana zaman tahiyya da iklasi tare da fata, yana sallamewa da rahama da kwadayi, yana juyawa daga sallar da tsoro da fata, idan ya aikata haka to ya sauke sallah da hakikaninta).

ثمّ قيل : ما أدب الصلاة ؟ قال  :

«حضور القلب وإفراغ الجوارح ، وذلّ المقام بين يدي الله تبارک وتعالى ، ويجعل الجنّة عن يمينه ، والنار يراها عن يساره ، والصراط بين يديه ، والله أمامه ».

Sannan aka ce : mene ne ladubban sallah: sai ya ce: (halarto da zuciya da karkadewa da sallama gabbai, da kaskantuwa cikin tsayuwa a gaban Allah albarku da daukaka sun tabbatar masa, zai sanya aljanna daga daman sa da sanya wuta daga hagun sa sannan siradi kuma tsakankanin gaban sa, Allah kuma a gabansa)

ـ في صحف إدريس  :

«إذا دخلتم في الصلاة فاصرفوا لها خواطركم وأفكاركم ، وادعوا الله دعاءً طاهرآ متفرّغآ، وسلوه مصالحكم ومنافعكم بخضوع وخشوع وطاعة واستكانة ، وإذا ركعتم وسجدتم فأبعدوا عن نفوسكم أفكار الدنيا وهواجس السوء وأفعال الشرّ واعتقاد المكر ومآكل السحت والعدوان والأحقاد، واطرحوا بينكم ذلک كلّه ».

92- ya zo a cikin suhufu Idris (as): (idan kun shiga sallah ku sallama mata dukkanin nutsuwarku da tunaninku , ku roki Allah addu'a tsarkakka wacce aka karkade dukkanin zuciya daga wani abu, ku rokeshi maslahohinku da amfaninku da mika wuya da kankan da kai da da'a da talautuwa, idan kuka durkusa ruku'u da sujjada to ku nisanta dukkanin tunanin duniya da rayukanku da munana raye-raye da ayyukan sharri da kudurce makirci da cin haramun da kiyayya da gaba, kuyi watsi da baki dayan wadannan abubuwa daga tsakaninku.

ـ وفيما أوحى الله إلى موسى بن عمران  :

«عجّل التوبة ، وأخّر الذنب ، وتأنّ في المكث بين يديّ في الصلاة ».

 93- cikin abin da Allah ya yi wahayi ga Musa bn Imran: (ka gaggauta tuba, ka jinkirta zunubi, ka yi jinkiri cikin zama tsakanin gabana cikin sallah).[1]

Ina cewa wannan dan kadan kenan daga abin da ya kwarara daga ayoyin kur'ani da hadisai masu daraja da aka rawaito daga manzon muslunci da iyalansa tsarkaka, lallai malamanmu manya-manya Allah ya jikan wadanda suka gabacemu gidan gsakiya daga cikinsu ya kuma kare mana wadanda suka wanzu kuma Allah ya sakawa dukkanin su da alherin sa kan gudummawar su ga muslunci-hakika sun wallafa tarin litattafai cikin sanin ladubban badini na sallah da bayanin sirrikanta da yaye rufi kan kyawunta da kamalarta da girmamarta.

Bayan dukkanin wannan bayani da ya gabata shin akwai wani musulmi wanda zai wulakanta sallar sa da sakaci kanta, ko kuma ya zama bama ya yin sallar kan lokacinta ko kuma ma ya bar yin sallar-wa'ayazubillah Allah ya tsaremu sai ya kasance daga gayyar kafirai?

Ashe ba sallah bace mi'irajin muminai, guzurin masu tsoran Allah, fitilar salihai, munajatin masoya, kaffarar zunuban masu sabo, tsarkake zukatan masu zunubi, rahamar ubangijin talikai. Ginshikin addini da duniya, taken littafin musulmai, albarkar cikin kassai?...

Shin wanda yayi imani da Allah ya yi aiki nagari ba wajibi ne kansa ya tsayar da sallah?..

Tashi ka nemi kusanci zuwa ga ubangijinka da tsayar da sallah da tsantseni da takawa da iklasi, da tadabburi da zurfafa tunani, Iallai kai kana cikin hallarar Allah da dausayin sa da tsarkin sa, mala'iku na maka tsaraba da rahama d albarka da istigfari,lallai kai kana cikin kulawar Allah mai gani mai ji, yana son ya ji munajatinka cikin sallarka, kamar yadda kake son munajati da shi cikin sirrintawarka da bayyanawarka.

Ashe cikin zuciyarka da samuwarka baka ji wani sautin mai shela ba a bayyane yana fadin: (ku taho zuwa ga sallah) da muryar mai tada ikama yana fadin (kad kamat salat) hakika sallah ta tsayu.



[1] Mun nakalto mafi yawn wadannan riwayoyodaga littafin mizanul hikima shima daga biharul-anwar da wasa'il da kutubar araba'a da kanzul ummal da wasunsu ya tattaro sai ka neme su.