mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Me ake nufi cikin wannan hadisi: amma abubuwan da suke faruwa to cikinsu ku komawa marawaitan hadisanmu, lallai su hujjojina ne akanku, ni kuma hujjar Allah ne. Su wane ne Kenan? Maraji’ai Ko kuma marawaitan hadisi?

Salamu Alaikum
Abinda ya faru a zamani gaiba kubra, lallai imam ya kasance cikin fakuwa Allah ya gaggauta bayyanarsa, hakika ya maida mutane zuwa ga marawaitan hadisan A’imma amincin Allah ya tabbata garesu, yace:
(وأمّا الحوادث الواقعة فارجعوا فيها إلى رواة حديثنا، فإنّهم حجّتي عليكم، وأنا حجّة الله عليهم)،
Amma abubuwan da suke faruwa cikinsu ku koma zuwa ga marawaitan hadisanmu, lallai su hujjojinmu ne kanku, ni kuma hujjar Allah ne a kansu.
Haka ma imam Sadik (as) yana cewa:
وقال الإمام الصادق(عليه السلام): (من كان من الفقهاء صائناً لنفسه، حافظاً لدينه، مخالفاً على هواه، مطيعاً لأمر مولاه، فللعوام أن يقلّدوه)
Duk wanda ya kasance daga fakihai mai katange kansa mai kiyaye addninsa, mai sabawa son ransa, mai `da’a ga umarnin ubangijinsa, to ragowar amawa suyi taklidi da shi.
Mene ne abinda ake nufi daga wadannan kalamai da suka zo cikin wadannan hadisai?
Idan mun iya tabbatar da ingancinsa hadisan, to mene ne ake nufi da su ?
Maraji’ai ake nufi ?
Ko kuma marawaita hadisai ma’ana jakadun imam guda hudu su kadai ?
Shin a fikihu akwai wani dalili kan batun A’alamiyya ?
Mene ne dalili kan mujtahidanci da cewa shi mujtahidi na’ibin imam (Af) ne, sannan kamar yadda muke fadi ko wasu malamai suke fadin cewa duk wanda yayi masa martani ya yiwa Allah martini.
Shin akwai wani nassi da yake bashi wannan siffa?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Abinda ake nufi daga wadannan kalamai su ne fakihai masu girma wadanda suka kasance sun tattaro sharuddan taklidi kamar yadda aka ambata cikin risalolin aiki, amma A’alamiyya dalili kanta hankali ne da hankalta, lallai shi mutum yana komawa ga kwararren likita mafi hazaka tare da cewa yanada tare da hazikin likita.

Amma dalili kan na’ibanta gamammiya shi ne abin da ya gangaro cikin riwayoyi wacce kai da kanka ka kawo guda biyu daga ciki, sannan idan kana bukatar bayani dalla-dalla filla-filla to sai ka komawa littafinmu mai suna : (kaulul rashid fi ijthadi wat taklidi) wanda mujalladi uku ne sannan an sauke a sayit dinmu.

Tarihi: [2018/1/20]     Ziyara: [843]

Tura tambaya