mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ina fama da matsalar zamewar zuciya daga hanyar gaskiya

Salamu Alaikum. Sayyid ni ina fama da matsalar karkatar zuciya da yawan wasiwasi, ina bakin iyawata don ganin na kubuta daga wannan matsala sai cewa hakan bai bada wata fa’ida ba, kowacce rana sai karuwa abin yake ta yanda ya kai ga sanya jin kasala lokacin ibada da rashin samun nutsuwa cikin salla sai kaga tunanunnuka marasa kyawu da rashin Imani da samuwar Allah suna bijiro mini, ina fatan zaku taimake ni da wani abu. Allah ya saka muku da alherinsa.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Sarkin muminai Ali (as) lokacin da yakewa `dansa nasiha yace masa: ya kai `dana kayi aiki cikin nishadi da lokacin kasala.

Bawai kawai kasala cikin ibada ba kadai bari dai dukkanin kasala sawa’un lokacin karatu ne ko kasuwanci ko sana’a, cikin abinda ya ta’allaka al’amuran dangi da al’umma cikin kowanne hali a zage ayi aiki tukuru da sannu zaka samu galaba kan kasala.

Allah ne mai bada taimako.  

Tarihi: [2019/3/17]     Ziyara: [515]

Tura tambaya