mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Na yi auren mutu’a tareda wani mutumSalamu Alaikum. Na yi auren mutu’a da wani mutum kuma mun cimma daidaito tareda ayyana sadaki sai dai cewa lokacin kullawa sai ya kasance bai lazimci abinda muka ittifaki kai ba bai bani sadakina ba, tambayata anan shine menene makomar wannan aure shin ingantacce ko kuma ya baci


Salamu Alaikum. Na yi auren mutu’a da wani mutum kuma mun cimma daidaito tareda ayyana sadaki sai dai cewa lokacin kullawa sai ya kasance bai lazimci abinda muka ittifaki kai ba bai bani sadakina ba, tambayata anan shine menene makomar wannan aure shin ingantacce ko kuma ya baci?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Aurenku bai da wata matsala sai dai cewa shi mijin ya aikata sabo da zunubi, a wurin mu dukkanin wanda ya kuduri niyyar cewa bazai bada sadaki ba a auren da’imi ko na mutu’a daidai yake da barawo kai hatta kusantarki da yake shi yana da hukuncin zina Allah ya tsaremu, ya zama dole ayiwa wannan mutumi nasiha da nusantar da shi don ya san hukuncin shari’a.

Allah nai mai taimako.

Tarihi: [2019/3/14]     Ziyara: [598]

Tura tambaya